Daura Multi-Disciplinary Journal Logo
DAURA MDJ YBUCOELS Daura, Katsina State
Current Issue Volume 4 Number 1 November 2026 • ISSN: 2672-4359

Vol. 4 No. 1 (November 2026)

Yusuf Bala Usman College of Education and Legal Studies, Daura, Katsina State

A collection of studies focused on the preservation of indigenous Nigerian languages, oral literature archiving, and historical discourse analysis.

Daura Logo
DMJGS
18 Articles Published

Table of Contents

Peer Reviewed • Diamond Open Access • Multi-Disciplinary
Advance Search
Hausa Pages: 1–15
Open Access (CC BY 4.0)

BA A MAGANCE BARNA DA BARNA: NAZARIN MATSALOLIN ZANGA-ZANGA A CIKIN WASU RUBUTATTUN WAQOQI NA HAUSA

Ibrahim Baba (Nayaya) (Yusuf Bala Usman College of Education and Legal Studies, Daura) ; Da Danlami Bala Gwammaja (Yusuf Bala Usman College of Education and Legal Studies, Daura) ; PhD Da Binta Bala Kwaru (Yusuf Bala Usman College of Education and Legal Studies, Daura)
Show Abstract & Keywords

Duk wani abu da ya faru, mai kyau ne ko akasin sa, to akwai dalili! Tabbas haka
abin yake a zamantakewar rayuwar al’umma. Wata rana, rayuwa ta yi fari, wata
rana kuma ta yi baqi. A wannan takarda, ta yi qoqarin fito da bayanai a kan
zanga-zanga daga cikin wasu waqoqin Hausa rubutattu. A binciken, an yi
qoqarin nazartar waqoqi guda biyu, inda a cikinsu aka zaqulo wasu baitukan da
suka yi Magana a kan sabuban zanga-zanga, da hasashen yadda ake gudanar da
zanga-zanga, sannan da matsalolin da zanga-zanga kan iya haifarwa. A takardar,
an fara bijiro da ma’anar waqa da taqaitaccen tarihinta, sannan aka biyo baya da
tarihin samuwarta. Har wa yau dai, binciken ya zo da bayani a kan ma’anar
zanga-zanga, raberabenta da kuma illolinta, inda takardar ta fi mayar da hankali
a kan zanga-zangar da ba ta lumana ba. A yayin gudanar da binciken, za yi
qoqarin bin ayyukan masana waxanda suka jivinci wannan aiki, da kuma kallon
yanayin da ake ciki, tare da bibiyar al’amuran tsaro da tsadar rayuwa. Babbar
manufar takardar dai, fito da zahirin rayuwar al’umma daga cikin ayyukan
adabi, da kuma nuna yadda adabi ya zama haske ga rayuwar al’umma kai tsaye.
A qarshen takardar, an bayyana sakamakon da binciken ya gano, sannan aka zo
da kammalawa. An xora wannan aiki a kan ra’in Mazahabar Nason Adabi a
Aladu (Folk-Cultural Theory) wadda William Bascom (1912 – 1981) ya qirqira.

Keywords: Magance, Varna, Matsaloli, Zanga-Zanga, Sababi, Rubutattun Waqoqi
12 views 9 DLs 0 cites
Hausa Pages: 35–46
Open Access (CC BY 4.0)

NAZARI A KAN KIRARIN ABINCIN HAUSAWA

AHMED ALIYU Ph.D DA SALIHU ILIYASU SULLUBAWA Ph.D (Yusuf Bala Usman College of Education and Legal Studies, Daura)
Show Abstract & Keywords

A cikin kowace al’umma abinci da tufafi da muhalli na daga cikin abin tinqaho da su,
al’ummar
Hausawa mutane ne masu riqo da al’adunsu na gargajiya, musamman wajen waxanda suke
gudanarwa a rayuwarsu ta yau da kullum. Hanyar da aka bi wajen gudanar da wannan
bincike sun haxa da, tattaunawa da mutane da karantowa daga rubutattun
bayanai. Qudirin wannan takarda shi ne ya binciko tare da tattaro bayanai a kan kirarin
abinci na Hausawa tare da tattaunawa ko rarrabe tsakanin aya da tsakuwa, ganin yadda
yawanci abinci gargajiya ke neman zama tarihi a idanuwan Hausawa sakamakon cuxanya
da wasu al’ummomi na kusa da na nesa, kamar Larabawa da Turawa da Fulani da Buzaye
da Nufawa da kuma Yarabawa da sauransu. Daga qarshe, an gano cewa akwai kirari
cunkushe a cikin abincin Hausawa na gargajiya da zaka tarar suna yi domin havaka harshe
da kuma raya al’adun Hausawa.

9 views 8 DLs 0 cites
Hausa Pages: 116–127
Open Access (CC BY 4.0)

NAZARIN BAMBANCIN MA’ANAR KALMA A MUHALLIN MAGANA. A BISA RA’IN MICHAEL HALLIDAY (1985)

Salihu Iliyasu Sulluvawa (Yusuf Bala Usman College of Education and Legal Studies, Daura)
Show Abstract & Keywords

Wannan bincike ya yi nazari ne kan yadda ma‘anar kalma ke sassauyawa dangane da muhallin magana. An gina wannan bincike a kan ra‘in Halliday na (1985) na Systematic Functional Linguistics (SLF). Muqalar ta yi bayani ne game da yadda mahallin magana ke tattance ma‘anar kalma. Manufar wannan binciken ita ce bayyana abubuwa uku na fage da alaqar masu magana da kuma salon isar da saqo. Hanyoyin da aka bi don tattara bayanai sun haxa da sauraro lokacin da ake magana, a matsayin ginshiqi (primary source of data) da kuma sauran bayanai da aka samu daga xakin karatu (secondary source of data). Sakamakon binciken ya gano cewa amfani da kalma a mahallin magana, nan ne ma‘anarta ke fita.

Keywords: Halliday, Kalma, Muhallin magana, Ma‘anar kalma, Ra‘i
10 views 9 DLs 0 cites